Tsige Gwamna Buni: Jam’iyyar APC ta Allah Wadai da Karar da PDP ta Shigar

 

Jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a Najeriya tayi Allah wadai da kiraye-kirayen a tsige shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni.

Mai magana da yawun jam’iyyar James Akpanudoedehe ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta.

Akpanudoedehe ya bayyana matakin kotun a matsayin mara ma’ana kuma wanda bai dace ba, yana mai cewa babbar jam’iyyar adawa tana cikin mawuyacin hali.

Abuja – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi Allah wadai da karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar akanta da shugaban kwamitin rikonta, Gwamna Mai Mala Buni.

A cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, mai magana da yawun jam’iyyar, James Akpanudoedehe, ya ce babbar jam’iyyar adawa tana aiwatar da farfaganda mara kyau.

Kodayake ya bayyana cewa APC ba za ta yi magana kan matakin zuwa kotu da PDP ta dauka ba, amma ya nemi jam’iyyar adawar da ta mayar da hankali kan rikicin da ke cikin sansaninta.

A cikin takardar sammaci mai shafuka hudu da aka shigar a kotun a ranar Alhamis, an bukaci kotun da ta sa gwamnan ya bayyana a gabanta tare da kare ko ya tashi daga matsayin gwamna ta hanyar yarda ya zama Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here