Adadin Karin Malaman Firamare da Sakandire da Afrika ke Bukata Kafin 2030
Kasashen kudu da hamadar saharar Africa za su bukaci karin malaman firamare da sakandare miliyan 15, kafin shekara ta 2030 domin raya fanin ilimi da annobar corona ta yiwa nakasu.
Read Also:
Majalisar Dinkin Duniya ta shaida hakan ne a wanan rana da ake bikin ranar malamai ta duniya, tana mai cewa akwai bukatar sake hubbasa domin sake farfado da bangaren ilimi.
Ana bikin ranar ɗalibai a ranar 5 ga watan Oktobar kowacce shekara domin tunawa da gudunmawa malamai a fanin ilimi a duniya baki daya.
Sannan ranar kan mayar da hankali wajen duba matsalolin malamai da bijiro da hanyoyin sake inganta musu rayuwa.