Nan da ƙarshen Mako Man Fetur Zai Wadata a Ko’ina – Gwamnatin Najeriya

 

Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri ya ce daga yanzu zuwa ƙarshen mako man fetur zai wadata a ko’ina a faɗin ƙasar.

Ministan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawarsa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a fadar shugaban ƙasar.

Ministan ya ce shugaban ƙasa ne ya buƙaci mataimakinsa ya kira taron na gaggawa domin sanin halin da ake ciki a game da batun man fetur.

A ranar Talata ne kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin litar mai daga naira 617 zuwa naira 897.

“Abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne akwai man, sannan muna da yaƙinin nan zuwa ƙarshen mako zai wadata a ko’ina a faɗin ƙasar nan.”

Ya ƙara da cewa farashin zai bambanta a wurare, “amma mun yi amannar cewa idan ya wadata, dole farashin zai ragu sosai.”

Ministan ta kuma bayyana cewa shugaban ƙasa ya damu da halin da ƴan Najeriya suke ciki, inda ya ce hakan ne ma ya sa ya umarci mataimakinsa ya kira taron domin tattaunawa da kuma neman mafita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here