Shugaban Kasar Syria ya Zargi Kasashen Yamma da Tayar da Yakin Ukraine
Shugaban Syria Bashar al-Asad ya zargi kasashen yamma da tayar da yakin Ukraine.
“Kasashen yamma na fakewa da taimakawa al’ummar duniya, amma a lokaci guda kuma suna aikata laifukan yaki ga al’umar duniya,” kamar yadda Bahsar al-Assad aka ambato shi yana fada.
Read Also:
Kamfanin dillancin labarai na Syria ya ambato shi yana cewa, “kasashen Turai ba za su iya yaudarar Syria ba, duk da fake wa da cewa suna taimako cikin gwammai, kuma wannan ba karamin abin abu ba ne mai mahimmanci.”
“Kasashen yamma na nunawa suriya tsana a fili tare da mutanenta, amma abin da yake faruwa a Syria ya tilasta musu bayyana abin da suka dade suka boyewa a ransu, kuma abin da yake faruwa yanzu a Syria ya kara nuna inda suka dosa a fili,” in ji Bashar al-Assad.
Ya ce yakin Syria ya yi wa kasashen Yamma tsirara, na farko daga mutane yamma na biyu ga sauran mutanen duniya.