Mun Kashe ‘Yan Ta’adda 52 da Kama 53 a Jihohin Borno da Yobe – Sojoji

 

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 52 da kama 53 a wasu samame da suka kai jihohin Borno da Yobe.

Mai magana da yawun hedkwatar sojojin, Manjo-Janar Edward Buba, shi ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, inda ya ce ƴan ta’adda bakwai da suka haɗa maza biyar da mata biyu sun miƙa kansu ga sojojin.

Janar Buba ya ce an kuɓuto da mutum 61 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban da ke ƙasar.

Ya kuma ce dakarun Operation Haɗin Kai a yankin arewa maso gabas, sun yi artabu da ƴan ta’addan a lokacin da suka kai samame, inda suka samu nasarar ƙwato makamai da dama.

A ɗayan ɓangare, ya ce dakarun Operation Delta Safe sun samu nasarar kama masu satar ɗanyen man fetur, inda suka kwace lita 496, 250 na ɗanyen mai, injunan tuka-tuka guda huɗu, jiragen ruwa biyar da tankunan ajiye mai 57 da sauransu.

Janar Edward ya ce baya ga wannan, sojojin sun kwace harsasai daban-daban daga wajen masu aikata ta’asar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com