Ba Mata ne Kawai ke Shan Maganin “INFECTION” ba…

 

Akwai wata matsala da “Matan Aure” ke fuskanta idan suna fama da cutar Infection(wato cutar da Al’umma ke kira da “Toilet Infection”). Wannan gagarumar matsalar itace; mazajen su na “Aure” sau da yawa kan ‘ki shan magani idan Matan sun zo asibiti akan cutar(STI’s). A mafi akasari “Likita” kan bu’kaci Mata da Mijin kowa ya sha maganin cutar. Amma abun takaici shine; Mazajen Aure da yawa ba sa bin wannan umarni na “Likita”.

Hakan kuma shi ke sakawa mata da yawa kullum suna cikin wannnan matsala ta “Infection”. Domin ko kin sha magani toh mijinki zai ‘kara saka miki wannnan cuta, saboda kuwa tana jikinshi sakamakon bijirewa shan maganin da Likita ya ce ya sha. Ya zama anyi ba a yi ba kenan! Amma na gano cewa sau dayawa abun da ya sa maza su ke ‘kin shan maganin shine; wasu ba sa jin alamomin cutar infection din a jikinsu, shi ya sa sai su ‘dauka kamar ba sa ‘dauke da cutar. Maganar gaskiya ya zama dole ku dinga shan magani duk sadda “Likita” ya ce a yi hakan.

Amma mene shawarar ku ga irin wadannan mazajen?

Tambihi: Dan Allah mu dinga yiwa Mata Adalchi wajan kula da lafiyar jikinsu. Hakan ya na da matu’kar muhimmanci a cikin rayuwar su da rayuwar mazajen su.

Dr Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Mai Wayar Da Al’umma Kan Cututtuka Da Dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com