Tankar Man Fetur ta yi Sanadin Mutuwar Mutane 34 a Benin

 

Gwamnatin Benin ta ce aƙalla mutum 34 ne suka mutu bayan da wata motar dakon man fetur ta kama da wuta a kudancin ƙasar.

Ministan cikin gida na kasar Alassane Seidou ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a garin Seme Podji kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 34 ciki har da jarirai biyu”, in ji shi.

Gawarwakin mutanen sun ƙone sakamokon wuta da hayaƙin da suka turnuƙe wurin da lamarin ya faru.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com