Gwamna Dauda ya Haramta Haƙar Ma’adinai ba Bisa ƙa’ida ba a Faɗin Jihar Zamfara

 

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya haramta dukkan ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar, inda ya buƙaci jami’an tsaro su ɗauki tsauraran matakai kan waɗanda suka yi biris da umarnin.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ranar Asabar ya ce gwamnatin jihar ta lura cewa aikin haƙar ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba ya taka rawa wajen ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a jihar.

Gwamna Dauda ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ɗaukar matakai da za su kare lafiyar mutane.

“Na bai wa jami’an tsaro umarnin harbi kan duk wanda aka samu yana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

“Mun ɗauki matakin ne don tabbatar da lafiyar al’ummar Zamfara da kuma jan kunnen masu aikata irin wannan laifi,” in ji gwamnan.

Dauda ya kuma ce sun ɗauki matakin ne domin ganin albarkatun jihar sun dawo ƙarƙashin ikon gwamnatinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com