An Kashe Mijin Marigayiya Farfasa Dora Akunyili, Dr Chike Akunyili

 

An kashe Dr Chike Akunyili, miji ga tsohuwar Shugabar Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta NAFDAC, marigayiya Farfesa Dora Akunyili.

An kashe shi ne tare da wasu mutane bakwai yayin wani hari da ‘yan bindiga suka kai garin Nkpor da ke karamar hukumar Idemili a jahar Anambra.

Ganau sun bayyana cewa maharan sun rika fadar cewa “ba za a yi zaben Anambra ba a watan Nuwamba.”

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jahar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu ya ce har yanzu ba su gama tattara bayanai kan harin ba.

Ana samun rahotannin hare-hare a yankin kudancin Najeriya musamman yankunan da kungiyar masu rajin ballewa daga Najeriya ta IPOB suke.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here