Mutanen Yankin Madamai da Kacecere da ke Jahar Kaduna Sun Koka da Rashin Tsaro

 

Jami’an tsaro a kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf na jahar Kaduna sun sake gano gawawwaki 3 a yankunan.

Tuni mazauna kauyukan Madamai da Kacecere suka fara tattara komatsansu inda suke gudun hijira zuwa birni.

Sun koka da halin da suka tsinci kansu inda suke kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki da gaggawa.

Kaduna – A ranar Talata, jami’an tsaro sun kara samo gawawwaki uku a kauyukan Madamai da Kacecere da ke kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf, lamarin da yasa yawan mamatan ya kai har arba’in da biyar.

Daily Trust ta tattaro cewa, za a yi birniyar wasu daga cikin mamatan a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura a ranar Alhamis yayin da aka birne wasu kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Litinin a karamar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Talata ya ce rahotannin tsaro sun bayyana cewa an sake samun karin gawawwaki 3, biyu daga harin Madamai, daya kuma a harin Kacecere. Kamar yadda Aruwan ya ce, ana cigaba da ayyukan nema tare da ceto wasu.

Amma kuma Daily Trust ta gano cewa, wadanda suka sha da kyar daga harin Kacecere sun tsere zuwa Zangon Kataf domin neman mafaka.

Shuaibu Tanimu, daya daga cikin wadanda suka tsallake harin da baya sun sanar da Daily Trust cewa sun bar gidajensu domin tserar da rayukansu duk da mutum hudu sun bace.

Wani mazaunin kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura, Derek Christopher, ya ce da yawa daga cikin mazauna yankin sun rasa gidajensu sakamakon hare-haren. Sun koma yankunan kusa saboda babu sansanin ‘yan gudun hiijira.

A yayin bada labarin abinda ta fuskanta, tsohuwa mai shekaru 79 a Zangon Kataf wacce ta bada sunanta a Habiba Ibrahim, ta ce miyagun sun tsinke mata hannunta da adda inda suka bar ta cikin jini.

Ta sanar da cewa an fara kai ta asibitin tunawa da Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan, kafin daga bisani a mika ta wani asibiti da ba a bayyana ba tare da wasu mutum hudu domin samun taimakon likitoci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here