Sabon Hari: An Kashe Mutane 16 a Jihar Benue
Wasu tsagerun yan bindiga dadi sun sake kai hari jihar Benue kuma an yi rashin rayuka 16
Shugaban karamar hukumar da aka kai harin yayi zargin cewa makiyaya ne suka kai musu hari.
Har ila yau, jihar Benue da wasu jihohin Najeriya na fama da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Benue -Akalla dilolin katako timba guda goma sha shida suka rasa rayukansu a sabon harin da yan bindiga suka kai Mbagwen a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Read Also:
Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, wanda ya tabbatar da kisan yace kimanin karfe 7 na yammacin Litinin yan bindiga suka kai hari garin Mbagwen kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi, rahoton Leadership.
Yace:
“An kashe dilolin timba 16, mun tsinci gawawwaki biyar cikin mutum 16.”
“Mafi akasarin wadanda aka kashe dilolin Timba ne a ranar Litnin yayinda suka je yankar itace a dajin Mbagwen kuma yayinda suke kokarin fita aka bude musu wuta.”
Ya ce sun kai kara wajen yan sanda don gudanar da bincike kan lamarin.