2022 World CUP: Hukuncin da Gwamnatin Qatar ta Tanadar wa Duk Wanda ya Aikata Zina Ko Luwadi

Gwamnatin kasar Qatar tace a gasar kwallon kafar duniya ta bana, ba zata yarda da fasadi da lalaci ba.

Qatar kasar Larabawa ce kuma an kafa dokoki haramcin Zina, shaye-shaye da casu ga kowani mutum.

Kwamitin koli da ta shirya gasar ta bayyana cewa ko kadan ba za’a canza dokokin addini don gasar kwallo ba.

An gargadi masu niyyar halartan gasar kwallon duniya da za’a yi a kasar Qatar bana cewa duk wanda aka kama yana zina zai iya shiga kurkukun shekaru bakwai.

Hakazalika an hana shan giya a bainar jama’a kamar yadda ake yi a wasu kasashe.

Gwamnatin kasar Larabawar ta Qatar ta bayyana cewa ko kadan ba zata canza dokokinta na addinin Islama ba don wani gasar kwallo.

Hukumomi a kasar Birtaniya sun fara kokawa kan yiwuwar takurawa yan kasarta dake niyyar zuwa Qatar kallon wasannin kwallon.

Wata majiya ta yan sanda ta bayyanawa DailyStar cewa:

“Idan ba miji da mata masu aure ba, basu yarda mutum yayi jima’i ba. Hakazalika babu casu gaba daya. Kowa ya fahimci haka ko kuma a jefashi kurkuku.”

“Yan kallo su shirya, babu jima’i da zinace-zinace wannan karon.”

Zina da luwadi haramun ne a kasar Qatar, kuma duk wanda aka kama zai iya kwashe shekaru 7 a daure.

Shugaban kwamitin tsare-tsaren gasar kwallon FIFA 2022 World Cup, Nasser Al-Khater, ya bayyana cewa:

“Abinda yafi muhimmanci garemu shine tsaron lafiyar kowani dan kallo. Amma rungume-rungume ba al’adarmu bace – kuma wannan ya shafi kowa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here