Bincike: A Cikin Wata Bakwai an Kashe Mutane 3,478 a Fadin Najeriya
Akalla mutum 3,478 aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da 2,256 a Najeriya daga watan Disambar 2021 zuwa watan Yunin 2022.
Jaridar Punch ta ambato wasu alkaluma daga cibiyar nazari da binciken lamuran tsaro ta Nigeria Security Tracker, wadda ta tattara jerin hare-haren da suka faru daga watan Disambar bara zuwa yanzu.
Kamar yadda rahoton ya nuna, a watan Disambar 2021 an kashe akalla mutum 342 yayin da aka yi garkuwa da 397 da suka hada da manoma 45 a jihar Nasarawa.
Read Also:
Rahoton ya kuma nuna cewa a watan Janairu an kashe akalla 844, yayin da aka yi garkuwa da wasu 603.
Sanannu daga jerin hare-hare a watan su ne na jihar Zamfara da Neja, inda aka kashe sama da mutum 400 a tsakanin jihohin biyu.
Nigeria Security Tracker ta kuma gano cewa mafi yawan hare-haren da mutanen da aka kashe a Arewacin kasar ne, duk da a Kudancin kasar ana zargin Kungiyar yan Awaren IPOB da aikata kashe kashe.
Amma a Arewaci an fi zargin barayin daji da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Neja.