Ahmad Lawan ya Shiga Zaben Fidda Gwani na Neman Sanata a Yobe – Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Ahmad Lawan ya shiga zaben fitar da gwani na neman takarar kujerar Sanata a Yobe ta Arewa da jam’iyyar ta gudanar.

Jaridar The Nation ta ambato Sanata Adamu yana yin wannan kalami a lokacin da ya jagoranci wasu ‘yan jam’iyyar zuwa fadar Shugaba Muhammadu Buhari, domin gabatar da zababben gwamnan Jihar Ekiti Biodun Oyebanji.

Sai dai mutumin da ke ikirarin lashe zaben, Bashir Machina na ci gaba da bayyana cewa Sanata Ahmad Lawan bai shiga takarar Sanata a Yobe ba, ya shiga takarar shugaban kasa ne.

Rahotanni sun ce Machina ya yi barazanar maka jam’iyyarsa kotu, bayan da wasu bayanai ke cewa sunan Ahmed Lawan aka mika wa hukumar zabe ta INEC a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar APC takara daga Yobe ta Arewa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here