Wurin Haƙar Zinare: An Kashe Mutane 4 a Harin ‘Yan Tawaye a Congo

Mutum huɗu ciki har da ƴan ƙasar China biyu aka kashe a wani harin yan tawaye a wani wurin haƙar zinare a arewa maso gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Wani mai magana da yawun sojin ƙasar ya ɗora alhakin kai harin kan wata ƙungiyar haɗin kai da ci gaban Congo mai suna CODECO inda aka kai harin a Damblo da ke lardin Ituri.

Watanni shida da suka gabata, Felix Tshisekedi ya sa an yi ƙawanya a lardin Ituri da lardin Kivu mai makwaftaka – wanda wannan wani yunƙuri ne na ƙara wa sojoji ƙarfi. Duk da wannan matakin da gwamnati ta ɗauka, an ci gaba da kisan kiyashi da kuma garkuwa da mutane.

Ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama na ƙasa da ƙasa ciki har da ƙungiyar Save The Children da Norwegian Refugee Council duk sun bayyana cewa wani sabon nau’in hare-haren ƴan tawaye ya sa sun rage ayyukan da suke yi a Ituri, lamarin da ya ja dubu ɗaruruwan mutane ba su samun agaji.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here