Za mu Kashe N863bn Don Yaƙar Talauci – Gwamnatin Shugaba Buhari
Gwamnatin Najeriya za ta kashe naira biliyan 863 wurin gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma na karshen shekara.
Shirye-shirye ne na musamman da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo dasu da nufin rage wa yan kasar radadin talauci.
Read Also:
Shirin National Social Investments Programmes (NSIP) da ya kunshi shirin N-Power da Conditional Cash Transfer Programme (CCT), da kuma shirin raba basussuka ga kananan yan kasuwa zai lakume naira biliyan 410.
Za a kuma kashe karin naira biliyan 300 kan wasu shirye-shiryen na daban ga al’umma.
Tun a shekarar 2016 ne gwamnati mai ci a Najeriya ta bullo da shirye-shiryen tallafa wa yan kasarta don rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.
Kuma a 2020 abubuwa sun dada nauyi ga yan Najeriya bayan bullar annobar corona, da ta yi illa ga tattalin arziki.