A Nahiyar Afrika, Kashi 40 ne Suka yi Cikakkiyar Rigakafin Cutar Corona – Hukumar Lafiya ta Duniya
Hukumar lafiya ta duniya ta ce kasashen Afurka 14 ne kacal suka yi wa sama da kasha 10 cikin 100 na al’ummarsu rigakafin cutar corona duk da tarin jama’ar da suke da ita.
Read Also:
Cikin kasashen Seychelles, Mauritius da Morocco ne kadai suka yi rawar gani, inda suka yi wa kasha 40 cikin 100 rigakafin cutar.
Baki daya dai a nahiyar Afurka, kashi 40 ne suka yi cikakkiyar rigakafin cutar corona, idan aka kwatanta da kasha 60 na Tarayyar Turai.
Manufar shirin Covax dai shi ne taimakawa kasashe masu karamin karfi da allurer rigakafin korona kusan miliyan dari 3, said ai hakan ba ta samu ba sakamakon yadda kasashe masu karfi suka saye ta.