Shugaban Hukumar NITDA, Malam Kashif Ya Ɗauki Nauyin Koyawa Masu Buƙata Ta Musamman Sana’o’in Dogaro Da Kai
A ƙoƙarinsa na ci gaba da samarwa ɗimbin al’ummomi daban-daban hanyoyin dogaro da kai, Shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, ya ɗauki nauyin mutane masu buƙata ta musamman kimanin su goma sha bakwai, (17).
An koya masu yadda ake ƙera takalman sawa na maza da na mata, da kuma yadda ake yin jakunkunan ado na mata, domin ganin sun tsaya da ƙafafunsu a cikin rayuwa.
Kimanin watanni shida aka yi ana horar da su, sannan kuma a cikin waɗannan watanni duk wata Malam Kashifu ya na bai wa kowane mutum ɗaya tallafin N5,000 domin su rage buƙatunsa saboda ba sa fita bara, su na zuwa ne wurin karɓan horon koyon sana’o’in su.
Bayan haka, Malam Kashifu ya ɗauki nauyin biyan malaman da su ka horar da su sana’o’in a cibiyoyi guda biyu da aka samar a Unguwar Mu’azu da kuma mazaɓar Dubantu, bisa jagorancin gidauniyarsa ta ba da agaji da taimakon al’umma, (Malam Inuwa Foundation).
A jawabin da ya gabatar a lokacin da su ka ziyarce shi domin yayewa da kuma godiya da yabo gare shi, Kashifu ya kuma ƙara da yi musu alƙawarin cewa zai kama masu shago zai biya masu kuɗin haya na tsawon shekaru biyu, zai kuma zuba masu kayan aiki kyauta domin su fara gudanar da sana’ar da su ka koya a matsayin kamfani, ta yadda za su yi ƙarfi su riƙe kansu su har su horar da wasu.
Daga ƙarshe kuma, sun gabatar masa da kyautar takalma kala biyu da jakar ado ta mata waɗanda su ka ƙera masa shi da iyalinsa bayan sun kammala domin nuna masa shaidar cewa lallai sun koya sun kuma ji daɗi matuƙa kuma a shirye su ke su yi riƙo da wannan sana’a sosai.
“Idan za ku riƙe wannan sana’a ku yi aiki tare a matsayin kamfani, sai kun kori masu ƙafar ma”. A cewar mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi.