Idan Kashifu ya ce ba Zai yi Takara ba Ina Kira ga Mutanen Jigawa su Kai Shi Kotu – Shugaban Kungiyoyin Arewa

Biyo bayan ɗumbin managartan ayyukan raya ƙasa da gina al’umma da ya yi tsawon shekaru uku a matsayin shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙungiyoyi daban-daban da ɗaiɗaikun jama’a daga ciki da wajen Jihar Jigawa na cigaba da yin kiraye-kiraye ga Malam Kashif Inuwa da ya fito neman takarar gwamna a (2023) a Jigawa.

A cikin wata hira da ya gabatar a gidan Rediyo Freedom, Bashir Goje Alade, wanda ke zaman shugaban gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na Arewacin Nageriya, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata ace al’ummar Jihar Jigawa sun matsa lamba wajen ganin Kashifu Inuwan ya amsa kiraye-kirayen da ake masa, idan kuma har ya ƙi to lallai jama’a su garzaya su maka shi a kotu domin shi ne mutum ɗaya tilo mafi cancantar ya gaji mai girma gwamna Badaru.

“Kashifu shi ne amsa ga al’ummar Jihar Jigawa, idan har ana son jam’iyyar APC ta ci zaɓe a 2023, ana kuma kishin Jihar Jigawa, to lallai a ba wa mai girma gwamna shawara ya ba wa Kashifu dama ya gaje shi. Kashifu kurman baƙi ne rubutun Allah, idan har aka ba shi takara to waɗanda ba ƴan jam’iyyar (APC) ɗin ba ma za su zaɓe shi. Haka zalika, Duk wani wanda ya ke tunanin APC ta ɓata masa to idan har an ce an ba wa Kashifu to kowa zai yi
domin Kashifu a wanke ya ke, tsarkakakke ne, bai saɓawa kowa ba, idan aka ba shi takara an ci an gama”. Inji shugaban ƙungiyoyin Arewan.

Bashir Aladen ya ƙara da bayyana wasu daga ayyukan alkhairan da Malam Kashif Inuwan ya aiwatar a Jihar Jigawa da tarayyar Nageriya, kamar samar da shirin ba da horo ga malaman makarantun sakandire a kowacce shiya ta Jihar Jigawa da gina cibiyoyin bunƙasa fasahar sadarwar zamani a kowane yankin Jihar, gami da samarwa matasa ayyukan dogaro da kai.

“Za mu shirya gangamin zanga-zangar lumana idan har Kashifu ya ce ba zai yi takara ba domin babu wani matashi da ya samu dama a Nageriya ya ke kuma amfanar da al’umma sama da shi. Mu kanmu mun kai masa ƙungiyoyin masu sana’o’i daban-daban kamar ƙungiyar mahauta da ta wanzamai an ba su horo na sana’o’insu kan fasahar zamani. Haka zalika kuma wannan lokaci ne da ya kamata a gwada matasa, a Jihar Jigawa Kashifu shi ne amsa, shi ne raba gardama, Mai girma gwamna da Allah ka ba wa Kashifu takara, ni kuma na yi alƙawarin duk inda na shiga zan ce a zaɓe ka a matsayin shugaban ƙasa”. Cewar Bashir Alade.

Daɗi da ƙari, wakilin ƙungiyoyin na Arewa, Comrade Bashir Alade, ya ƙara da cewa a matsayinsu na ƴan Arewa da ke jagorantar al’umma nauyi ne a kansu su haskakawa mutane abin da ya dace a kowacce Jiha, kuma su na da yaƙini da ƙarfin gwiwa akan Malam Kashif Inuwa idan ya samu damar zama gwamnan JIhar Jigawa (2023) zai bijiro da managartan tsare-tsaren da za su taimaka wajen ƙara bunƙasawa gami da ciyar da Jihar ta Jigawa gaba ta fuskoki daban-daban kamar yadda mai girma gwamna, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI) ya ke kan yi.

Garba Tela Haɗejia
Alhamis, 12 ga watan Maris, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here