Gwamnatin Katsina Za ta Ware Rabin Biliyan Don Tarban Buhari
Takarda ta bayyana yadda gwamnatin Katsina ke shirin kashe rabin biliyan don tarban Buhari.
Bincike ya nuna cewa wannan kudin na tara jama’a su tarbi shugaban kasa ne kawai ranar Alhamis.
Mabiya kafafen ra’ayi da sada zumunta sun bayyana takaicinsu game da yadda gwamnatoci ke kashe kudin al’umma.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da ya ware kimanin Naira milyan dari biyar domin tara jama’a don tarban shugaba Muhammadu Buhari a jihar.
Shugaban kasan zai kai ziyara ta musamman ranar Alhamis, 26 da Juma’a 27ga watan Junairu, 2023.
Gwamnan zai tsamo wannan kudi N499.6m daga asusun kananan hukumomin jihar, rahoton Leadership.
A cewar wata wasikar amincewa da kashe kudin mai kwanan wata 18 ga Junairu, 2023, wacce ta bayyana kafafen ra’ayi da sada zumunta, za’a fitar da kudi N14,695,588.00 ga kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomin jihar 34.
Read Also:
Sakataren din-din-din na gidan gwamnatin Katsina ya aike wasikar ga kwamishanan kananan hukumomi da lamuran sarakunan gargajiya.
Wasikar wacce wani Yahuza S Ibrahim ya rubuta madadin sakataren ya ce za’a yi amfani da kudin ne wajen tara jama’a don su yiwa shugaban kasa kyakkyawan tarba.
Yace:
“Bisa wasikarka mai lamba No. /MLGCA/GEN/259/C/IV of 17 January, 2023 An umurceni na sanar da kai cewa gwamna ya amince da fitar da kudi N14,695,588.00 ga kowace karamar hukuma, jimilla N499,650,000.00 daga kudin da ya rage cikin asusun kananan hukumomi 34 don tara jama’a su tarbi shugaban kasa a ziyarar da zai kawo jihar Katsina daga ranar 26-27 ga Junairu, 2023.”
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wannan kudi kimanin N500m na tattara jama’a ne kawai kuma bai kunshi kudin shakatawa, tsaro, da sauransu ba.
Tafiyar shugaba Buhari
Shugaba Buhari yanzu haka yana jihar Legas inda ya tafi kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Ayyukan sun hada da layin dogon jirgin kasa da kuma kamfanin sarrafa shinkafa.
Gabanin zuwan sa Legas, shugaban kasa ta je jihar Bauchi kaddamar da kamfen dan takaran gwamnan jihar, Air Marshal Sadique Abubakar.