Idan Na ci Zabe Zan Ruɓanya Nasarorin da na Samu Lokacin da na yi Gwamnan Kano – Kwankwaso

 

 

Dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan dadi ya ce Najeriya na fama da babban kalubale a bangaren ilimi.

Tsohon gwamnan yace idan ya zama shugaban ƙasa zai rubanya nasarorin da ya samu a jihar Kano.

Abuja – Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Kwankwaso, yace idan ya ci zabe zai ruɓanya nasarorin da ya samu lokacin yana gwamnan Kano.

Kwankwaso ya faɗi haka ne a Abuja ranar Litinin a wurin zauren al’umma na masu neman zama shugaban kasa, wanda tsangayar koyarda kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja ta shirya.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya koka kan yadda Najeriya ke fuskantar rikice-rikice a ɓangaren ilimi tun daga matakin karatun Firamare zuwa manyan makarantu.

Ɗan takarar jam’iyya mai kayan maramari NNPP ya bayyana cewa manyan jam’iyyu APC da PDP sun gaza, sun kunyata ‘yan Najeriya, kamar yadda jaridar Pumch ta rahoto.

“Ina farin ciki da jin daɗi ‘yan Najeriya suna da wani zabin bayan gazawar jam’iyyun APC da kuma PDP,” Inji Kwankwaso.

A cewar Sanata Kwankwaso, batun Ilimi batu ne mai matukar muhimmanci kuma idan ya zama shugaban kasa, gwamnatinsa zata shawo kan matsalolin daki-daki.

Kwankwaso ya ci gaba da cewa:

“A kundin manufofinmu, mun ce da zaran ka tsallake ka samu makin da ake bukata a jrabawar JAMB, zaka yi amfani da ita tsawon shekaru huɗu.”

“Bamu bukatar ka sake komawa ka zauna jarabawar saboda mun yi imani cewa tilas gwamnati ta ɗauki nauyin tabbatar da ‘ya’yanta maza da mata talakawa sun samu damarmakin zuwa Jami’a kamar saura.”

“Don haka abinda muka fi amanna da shi ne ilimi, ilimi da ilimi.”

Da yake jawabi, shugaban jami’ar UNIABUJA, Abdul-Rasheed Na’Allah, ya yi kira ga sauran masu neman kujerar shugaban kasa da su zo su gaya wa ‘yan Najeriya dalilin da yasa suke neman mulki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here