Hatsarin Mota ya yi Sanadiyyar Rasa Rayukan Fadawan Shehun Borno

 

 

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta tabbatar da cewa wani hatsarin mota ya rutsa da rayukan wasu faɗawan Shehun Borno guda uku, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kwamandan Hukumar a jihar ta Borno, Utten Iki Boyi, ya shaida wa Jaridar Daily Trust a Maiduguri da safiyar ranar Talata cewa mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, amma an ceto uku, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik lokacin da motar ta yi dungure sannan ta kama da wuta.

Ya ce nan da nan suka tura jami’an su zuwa wajen da lamarin ya faru, inda aka samu mutum uku sun ƙone kurmu har ba za a iya gane su ba. Sai dai ya ce an samu nasarar ceto mutum uku inda aka kai su zuwa babban asibitin Beneshiek don yi musu magani.

punch nigeria newspaper today

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here