Katsina: Gobara ta Barke a Babbar Kasuwar Jahar

Gobara ta barke a babbar kasuwar jahar Katsina wato Central Market da sanyin safiyar yau Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa, shaguna da yawa sun kone kurmus, yayin da ake kokarin kashe wutar.

Hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda sun hallara domin tabbatar da kiyaye dukiyoyin jama’a .

A safiyar Litinin din nan ne gobara ta kama a babbar kasuwar Jahar Katsina, wadda aka fi sani da Central Market, rahotanni na cewa an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a yayin lamarin.

An gano cewa wutar ta fara ne misalin karfe 8 na safe. kuma ta ci gaba da lalata shagunan da ke kasuwar, yayin da wasu da gobarar bata shafa ba ‘suka dunguma suka kwashe kayansu kafin wutar da ta tashi ta isa shagunansu.

Wakilin jaridar This Day wanda ya ziyarci kasuwar ya ruwaito cewa ba a iya gano asalin abin da ya faru da kuma yadda gobarar ta faro ba a lokacin hada wannan rahoto.

Amma gamayyar jami’an hukumar kashe gobara ta jahar Katsina, hukumar kashe gobara ta tarayya da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta jahar (SEMA) suna ta fafutukar kashe wutar. Rundunar ‘yan sanda na Najeriya, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), da Jami’an Tsaro NSCDC duk sun hallara a wurin don kula da tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here