Tabbas Zamu Kawo Karshen Rikicin PDP Gabanin Babban Zaɓen 2023 – Sanata Wabara

 

Muƙaddaahin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Wabara, yace tabbas zasu kawo karshen rikicin PDP.

Yayin ziyarar da suka kai wa gwamna Abiya, Wabara yace zasu yi duk me yuwuwa su tunkari babban zaɓe a inuwa ɗaya.

Gwamna Ikpeazu, yace tun farko kuskuren PDP ya jefa Najeriya hannun APC har aka shiga wannan yanayin.

Abia – Sanata Adolphus Wabara, muƙaddashin shugaban kwamitin amintattu (BoT) a jam’iyyar PDP ya tabbatar da cewa zasu kawo ƙarshen rikicin cikin gida da ya mamaye jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Wabara ya ba da wannnan tabbacin ne yayin da ya jagoranci mambobin BoT suka ziyarci gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya a mahaifarsa Umuobiakwa.

PDP ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu, wanda ya ayyana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a 2023.

A halin yanzu, Sanata Wabara yace zasu yi iya bakin kokarinsu don tabbatar da an lalubo ƙullin da kuma warware rikicin gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Bugu da ƙari, Yace kwamitin amintattu zai ziyarci gwamnoni da masu ruwa a tsaki da nufin dawo da zaman lafiyar da aka rasa a jam’iyyar PDP.

Kazalika, Wabara ya misalta gwamna Ikpeazu da mutum mai daraja wanda ake ganin girmansa a jam’iyya, inda ya kara da cewa ba za’a iya shafe gudummuwar da ya bayar ba wajen gina PDP.

Dole a nemi masalaha – Ikpeazu

Da yake nasa jawabin, gwamna Ikpeazu yace akwai buƙatar a zauna a nemo hanyar sulhu idan har dagaske ana son jam’iyyar ta kai labari a zaɓen 2023.

Yace akwai bukatar PDP ta sake nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan don kauce wa faɗa wa gidan jiya abinda ya auku a zaɓen 2015.

“Kuskuren mu ne ya kai ƙasar mu cikin wannan halin da take ciki a yanzu, ba don haka ba ai ba zamu faɗa hannun jam’iyyar APC ba.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here