Yadda Matashi Mai Shekarau 24 ya Mayar da Motarsa Zuwa Jirgin Sama Mai Saukar Ungula

 

Wani matashi ba’indiye mai suna Mithilesh Prasad ya sauya wata ‘yar motarsa zuwa jirgin sama mai saukar ungulu.

Matashin dan shekara 24 ya yiwa motar kare-karen jikin jirgin sama mai saukar ungulu, ya sauya baya da duk wasu bangarorin jikin motar.

Duk da a yanzu ya yi nasarar kirkirar jirginsa na sama, ya bayyana cewa, yana da burin wata rana ya gina cikakken jirgi.

Mithilesh Prasad, wani matashi mai shekaru 24 dan kasar Indiya ya baya da mamaki yayin da ya sauya motarsa zuwa jirgi mai saukar ungulu.

A wani rubutun Instagram da @trtworld ta yada, an ga yadda matashin ya yi ya cika burinsa na kera jirgi mai saukar ungulu.

Don tabbatar da motar tasa ta yi kamata da jirgi mai saukar ungulu, matashin ya yi sauye-sauye da dama, ciki har da lika bambam jirgi, farfela da dai sauransu. Sai dai, har yanzu jirgin bai fara tashi ba.

Wannan jirgi dai na samar wa Mithilesh kudin shiga ta hanyar ba da hayansa a lokutan bukukuwa, musamman aure.

Matashin ya ce yana da burin wata rana ya kera jirgi sukutum.

Martanin jama’a

@psean_the_artist yace:

“To ai zai iya yanke kan wani da wadannan farfelun.”

@thekhanarbab yace:

“Jira nike tun tuni naga jirgin ya fire, gazawarku ta kada ni TRT.”

@madebyeaq yce:

“Hanya mafi sauku wajen sheke mutanen da kake fushi dasu a kan titi.”

@hatebuster3300 yace:

“Na sha mamakin ba’indiye mai tallan abinci a bakin hanya yanzu kuma na gaza magana da ganin jirgi mara tashi da aka yi don biki.”

@f.ar.han_.sa.mi_ yace:

“Ya yi kusan irin abin da nake fatan yi. Aiki ya yi kyau dan uwa.”

@im.umar.qadri yace:

“Na tuna wani dan Indiyan da ya kera jirgi mai saukar ungulu, amma ya mutu garin gwada tashi Na tausaya masa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here