Hakkin Gwamnati ne Kawo Karshen Ta’addanci da ke Faruwa a Zamfara da Arewa ta Tsakiya – Bashir Magashi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa mulkinsa zai tabbatar da kulawa da rayuka da dukiyoyin su.
Ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce shugaban kasa ya bayyana wannan tabbacin ne a wani taro na tsaron kasa da suka yi a fadarsa da ke Abuja.
Magashi ya bayyana yadda shugabannin tsaro suka bayyana wa shugaban kasa halin da kasar nan ta ke ciki da sabon harin da aka kai wa jahar Zamfara.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya tabbacin sa na cewa mulkin sa zai tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin duk wasu ‘yan Najeriya ko menene matsayinsa a kasar nan.
Magashi ya bayyana hakan inda yace shugabannin tsaro sun kara bayyana halin da kasar nan ta ke ciki na rashin tsaro har da sabon ta’addancin da ya faru a jahar Zamfara da sauran jahohi na arewa maso yanma da arewa ta tsakiya da ke fadin kasar nan, Daily Nigerian ta rawaito hakan.
Read Also:
“An yi taron ne musamman don bayyana halin da arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ta ke ciki na matsaloli da sauran ta’addanci na garkuwa da mutane da sauran su.
“Daga taron, mun yarda da cewa hakkin gwamnati ne kawo karshen ta’addanci da ke faruwa a jahar Zamfara da arewa ta tsakiya.
“Mun tattauna a kan bukatar kawo karshen ‘yan ta’adda. Mun yarda da cewa suna kawo cece-kuce, hallaka jama’a, suna yin yadda suka ga dama kuma suna fadin abubuwan da suka so don su samu duk abinda suke so a hannun jama’a.
“Mun yarda da cewa muna iyakar kokarinmu na ganin mun dunkule kasar nan waje guda. Idan aka dubi shekarar 2014, za ka gane cewa an samu cigaba mai tarin yawa amma mutane ba sa ganin hakan.
“Gani suke yi kamar mun gaza ko kuma akwai wasu abubuwan da ba mu sani ba. Muna iyakar kokarin mu amma mutane ba sa ganin kokarin mu amma mutane ba sa ganin kokarin gwamnati.
“Mun san abinda muke yi kuma mun gane cewa za mu iya tsare Najeriya amma muna bukatar hadin kai. “Kamar yadda kowa ya sani duk kasar da babu tsaro ba za ta iya tabuka komai ba.
Don haka ya umarce mu da mu nemi hanyoyi da dabarun da za mu kawo karshen rashin tsaro kuma mun tabbatar masa da cewa za mu yi iyakar kokarin mu a kan lamarin,” a cewarsa