‘Yan Sandan Jahar Imo Sun Harbe Hatsabibin ‘Dan Fashi, Modukpe

 

‘Yan sanda sun kashe wasu hatsabiban yan fashi da makami biyu a jahar Imo.

‘Yan sandan sun kai samame ne mabuyar Modukpe, suka halaka shi bayan musayar wuta.

‘Yan sandan sun kuma kashe wani dan tawagar tare da raunta wasu da harsashin bindiga.

Imo – ‘Yan sanda a Imo sun ce sun bindige wasu hatsabiban ‘yan fashi da makami biyu, wadanda su da tawagarsu suka dade suna addabar mutanen garin Obiakpo a karamar hukumar Ohaji na jahar, rahoton Daily Trust.

Sanawar da kakakin ‘yan sandan jahar CSP Mike Abattam ya fitar ta ce ‘yan sandan bayan samun bayannan sirri sun kai samame mabuyar shugaban tawagar suka kashe shugaban, Modestus Ugwuoha wanda aka fi sani da ‘Modukpe’ da wani guda.

Ya ce sauran ‘yan tawagar sun tsere da raunin bindiga a jikinsu kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Ya kara da cewa jami’an yan sandan suna bin sahun sauran yan tawagar da suka tsere. A cewar Abattam, tawagar ce ta kitsa harin da aka kai ofishin yan sanda na Njaba tare da kashe jami’i mai mukamin sufeta.

Sanarwar ta ce:

“A ranat 6 ga watan Satumban 2021, misalin karfe 8 na dare bayan tattaro bayannan sirri, tawagar yan sanda na musamman sun kai samame mabuyar kungiyar yan ta’adda da suka dade suna adabar Obiakpo a karamar hukumar Ohaji Egbema a Jahar Imo.

“Da isar yan sandan, bata garin suka fara harbi, suka yi musayar wuta. Yan sanda sun yi nasara a kansu, an kashe biyu cikin bata garin yayin da saura suka tsere da raunin bindiga, an kuma kwato bindigu a hannunsu.”

Sanawar ta cigaba da cewa mutanen garin sun yi murnar jin labarin kashe Modukpe kuma bayanai sun nuna shine ya kitsa harin ofishin yan sanda na Njaba inda aka kashe sufetan yan sanda.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here