A cikin Shekara ɗaya tal Zamu Kawo Sauyi a Yanayin Tsaron Najeriya – Badaru da Matawalle

 

Ministocin tsaro, Muhammad Badaru da Bello Matawalle sun yi alkawarin kawo sauyi a yanayin tsaron Najeriya cikin shekara.

ɗaya Tsoffin gwamnonin sun shiga ofis a rana ta farko yau Talata awanni 24 bayan rantsuwar kama aiki.

Sun ce zasu yi duk mai yiwawa ba tare da gajiya wa ba wajen cika burin shugaban ƙasa da ‘yan Najeriya kan tsaro.

FCT, Abuja – Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, sun yi wa yan Najeriya alƙawari mai girma.

Sabbin ministocin biyu sun yi alkawalin kawo sauyi “na ban mamaki” a fasali da tsarin tsaron Najeriya a cikin shekara guda.

Badaru da Matawalle sun ɗauki wannan alkawari ne yayin da suke jawabi ga ‘yan jarida ranar Talata a ɗan kwarya-kwaryan bikin kama aiki da aka shirya musu a ma’aikatar tsaro da ke Abuja.

Channels tv ta tattaro cewa wannan na zuwa ne awanni 24 bayan Ministocin sun yi rantsuwar kama aiki.

Ba zamu ci amanar shugaba Tinubu ba – Badaru

Badaru, tsohon gwamnan Jigawa da ya gabata, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa saboda kasar nan, shi da karamin minista ba za su iya cin amanar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba su ba.

A cewarsa, a cikin shekara ɗaya tal, za a samu sauye-sauye na ban mamaki domin inganta harkokin tsaro a kasar nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma yi alkawarin cewa shi da Matawalle za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun fidda Tinubu kunya, wanda shi da ɗaukacin ‘yan Nijeriya ke da burin ganin an tabbatar da tsaro a lungu da saƙo na Najeriya.

A nasa bangaren, Matawalle ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen kafa matakan tsaro masu karfi da za su iya tunkarar duk wata barazana.

Kafin wannan muƙami da shugaba Tinubu ya naɗa shi, Matawalle ya riƙe kujerar gwamnan Zamfara, jihar da ake hasashen matsalar tsaro ta yi wa ƙatutu a Arewa maso Yamma.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com