Shehu Sani ya Shawarci Wike ya bi a Hankali Don Gudun Kar a Samu Matsala

 

Sabon ministan Birnin Tarayya (FCT) Abuja Nyesom Wike ya shiga ofis domin fara aiki.

Wike mamba ne a babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ake yi wa kallon mai son janyo hayaniya.

Dan jam’iyyarsa wato Sanata Shehu Sani ya ba shi shawarar ya bi a hankali don gudun kar a samu matsala.

FCT, Abuja – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya gargaɗi sabon ministan Birnin Tarayya (FCT) Abuja Nyesom Wike.

Ya ce Wike mutum ne jajirtacce a duk aikin da ya tasa a gaba, sai dai ya yi gargaɗin cewa zai iya janyowa kansa da Tinubu matsaloli masu girma.

Nyesom Wike dai na cikin mutane 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin ɗin da ta gabata domin su kama aiki a matsayin ministoci.

Shehu Sani ya shawarci Wike ya bi a hankali

Sanata Shehu Sani ya shawarci Wike da ya bi a hankali domin gudun kar ya takalo tsuliyar dodo kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, wanda ake kira da Twitter a baya.

Tsohon sanatan ya aminta da cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, wanda yanzu ya zama ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, ya san aiki sosai yadda ya kamata.

Sai dai ya shawarce shi da ya lura da irin kalamai da ayyukan da yake yi domin gudun kar ya jefa kansa da gwamnatin Shugaba Tinubu cikin rigingimu na siyasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com