Dalilin da Yasa na Kira Tinubu Shugaban Kasa – Abubakar Lado Suleja

 

Abubakar Lado Suleja, dan majalisar wakilai daga jahar Neja ya yi martani a kan wani bidiyo wanda a ciki ya kira Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin ‘Mai girma Shugaban kasa.

Lado ya bayyana cewa ya kira Tinbu da ‘shugaban kasa’ ne saboda shi suke fatan ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya kuma musanta ikirarin cewa ziyarar da suka kai ma jigon na APC yana nufin lamunce masa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Wani dan majalisar wakilai, Abubakar Lado Suleja (APC, Niger) ya yi bayanin bidiyon da ya shahara, wanda a ciki ya kira Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin ‘Mai girma Shugaban kasa’ a lokacin da suka ziyarce shi a Landan a makon da ya gabata.

Shugabannin kungiyoyin Arewa na APC, karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, sun ziyarci Tinubu a Landan a ranar 1 ga watan Oktoba.

A cikin bidiyon, Suleja ya cewa Tinubu yayin da ya yi kokarin shiga motarsa: “Mai girma Shugaban kasa, sai anjima.” Tinubu ya amsa da “Na gode.”

Suleja ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa ya kira Tinubu a matsayin Shugaban kasa.

Lokacin da aka tambaye shi ko yanzu kasar tana da shugabannin kasa biyu ne, sai ya ce:

“A’a, ba mu da shugabanni biyu, watakila ba ku saurari bidiyon sosai ba saboda lokacin da na ce Shugaban kasa, Insha Allah ya biyo baya, wanda ke nufin da yardar Allah. “Muna yi masa addu’an zama shugaban Najeriya na gaba.

Muna da shugaban kasa daya tilo wanda shine Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shine jagoran jam’iyyarmu kuma mai ba mu shawara amma muna addu’ar Asiwaju ya zama shugaban Tarayyar Najeriya na gaba kuma ya ci gaba daga inda shugaba Buhari zai tsaya. Abin da nake nufi kenan.

“Manufar ziyarar mu ita ce ganin yanayin lafiyarsa, yi masa addu’a da fatan alheri. Yana cikin koshin lafiya kuma kamar yadda kuke gani daga bidiyon, yana cikin yanayi mai kyau.

Ya kusan awa daya yana yi mana magana.” Suleja ya musanta ikirarin cewa ziyarar tasu ita ce ta amince da takarar Tinubu a matsayin shugaban kasa, PM News ta kuma rawaito.

“A’a, ziyarar ba don lamunce masa bane, mu masu biyayya ne, masoya kuma shi ne jagoranmu. Idan mutane na cewa don amince masa ne, to hakan na nufin Shugaba Buhari ya amince da shi saboda Shugaba Buhari ne ya fara ziyarar shi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here