Duk Masu  Kishin Ilimin Ƴaƴa Mata a Kano Dole su  ƙauna ci  Shirin AGILE

Hannatu suleiman Abba

Arewacin Najeriya na  sahun gaba a faɗin duniya wajen adadin yara marasa zuwa makaranta.

Hakan na zuwa ne bayan ƙididigar da Hukumar kula da yara  ta duniya wato UNICEF ta fitar inda kaso na  yara mara sa zuwa makaranta na da  yawa a arewacin Najeriya.

Shirin Adolescent Girls Initiative for learning Empowerment  (AGILE) na cikin Manyan Shirin da Bakin Duniya (world Bank) ya Kaddamar domin tabbatar da ya’ya mata sun samu ilimi Nagartatace da kuma Samar musu da hanyoyi dogaro da Kai bayan sun gama Makarantar sakandari.

Hakazalika, shirin AGILE ya zo da sabbin dabaru na tabbatar da  ilimi ya isa ga ƴaƴa mata a birni da karkara , inda suke mayar da hankali akan  gyara makarantun domin walwalar ɗalibai da Kuma samu muhallin da ke saka nutsuwa wajen ɗaukar darasi .

A kwanakin baya, kwamishina Ilimi na jahar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, a taron da  kafar yada labarai ta BBC Hausa suka shirya a Kano akan ilimi a jahohin uku na arewacin Najeriya wadanda suka hadar da Katsina ,Jigawa da Kuma Kano.

Doguwa cikin tinkaho,  ya bayyana cewa Gwammati Jahar Kano ke gyara Makarantar masu bukata ta mussaman Wanda take Tudun Maliki, inda a lokacin yayi izini da aje a tabbatar da abun da yake faɗa.

  Banyi kasa a gwiwa ba, saboda duk wanda yasan makarantar yasan yadda Gwamnati da dama ta shuɗe ba tare da gyara ko sabunta wasu Gine-Gine Da ke ciki ba.

Da shiga ta makarantar  sai naga tambarin AGILE a jiki Ajujuwa da aka gyara,Wanda gyara ya shafi duk makaranta. Dalibai cikin nutsuwa da walwalar suke karatu. Haka Kuma  yake, a duk makarantun sakandari  a kananan hukomomi 44  na jahar Kano, babu Inda za’a je ba ‘a ga Aikin AGILE ba,Wanda har Makarantun maza a shiga da tsarin gyaran.

Cikin bincike irin na aikin jarida da mukayi a kananan hukomomi  na cikin birni akan Aikin AGILE, wanda daga bisani muka tsallaka karkara, mu samu damar isa garin Tarda  Dake karamar Hukumar Ungogo, inda muka tarar Aikin gina bandakuna ga Ya’ya mata da Kuma yin bohal, ya taimaka musu sosai wajen fahimtar  tare da Samar da nutsuwa ga  karatu ɗalibai mata.

A cikin zantawa da Shugabar makarantar Mata ta Tarda Hajiya Rabi isma’il ta bayyana cewa , A  da inda ana cikin karatu dalibai mata  kan  bukaci shiga bandaki  Kuma  lokacin babu bandaki, dole su je Gidanje  su ko makwabta Dake jikin Makarantar, wasu ana suke samu damar kin  dawo wa  makarata don cigaba da daukar darasi.

  A dai cikin  Aikin da AGILE  ke yi akan ilimi Ya’ya mata a jahar kano, lokacin da Kungiyar Kano Ladies Mentors and Mentees Dialogue wato KALAMED, ta shirya taro akan bikin ranar ya mace na Duniya wato (International Girl child Day) a gari Takai a wanna shekara , AGILE ta bada tallafi domin a farantawa ya’ya mata da ke yanki tare da nuna musu muhimmaci Ilimi.

Akwai ƙungiyoyi dake zaman kansu a jahar Kano bisa sahalewar malamai da sarakuna da suke kare martabar Addini da al’ada ,  Shirin AGILE ya tabbatar suna cikin wanna tafiyar domin cigaban Jahar.

Wadannan kungiyoyi na  shiga karkara da Yan Jaridu domin kara nuna amfani  ilimi Yaya mata, wajen bayyana musu irin Gudunmawar da Shirin AGILE ke yi akan cigaba ilimi a  jahar Kano.

Wanda a haka yasa aka Kaddamar Shiri bada tallafi kudi ga dalibai mata domin rage tallace – tallace a lokaci karatu.

Hakazalika, a duk wata makaranta sakandari da AGILE ta yi aiki a ciki,  akwai   kwamiti din iyaye da malamai wato (P.T.A), Masu  unguwannin da sa sauran masu fada aji na yankin.

Kawo yanzu zamu iya cewa, Ilimi Ya’ya mata ya samu Gata a cikin Shirin AGILE, domin ya  rage kaso me yawa  akan Adadin da ake lissafawa na yawan samu  ya’ya mata marasa zuwa makaranta a Jahar Kano

Shirin AGILE Alkhairi ne ga karatu ya mace mussaman yaran da suka fito daga gidan marasa karfi a cikin al’umma.

Sanna Shirin AGILE ya bada damar bada shawarwari akan aikace-aikace da sukeyi, Inda ofishin su yake Gidan Murtala.

Hannatu suleiman Abba
[email protected].

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com