Birtaniya da Amurka Sun ba da Gargadi Game da ƙaruwar Barazanar Ta’addanci a Uganda

 

Babbar hukumar Biritaniya da ofishin jakadancin Amurka da ke Uganda sun ba da gargadi game da ƙaruwar barazanar ta’addanci a Uganda, musamman ga baƙi ‘yan kasashen waje.

Suna ba da shawarar hana halartar manyan tarukan da suka haɗa da ayyukan addini da bukukuwan kade-kade, yayin da shahararren bikin Nyege Nyege ke gabatowa.

Bugu da kari, gwamnatin Burtaniya ta shawarci ‘yan kasarta da su guji ziyartar wuraren shaƙatawa biyo bayan harin baya-bayan nan da kungiyar ‘yan ta’adda ta Allied Democratic Forces (ADF) ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ma’auratan Birtaniya da Afirka ta Kudu tare da jagoransu ɗan Uganda.

Uganda ta fuskanci ƙaruwar rashin tsaro, inda a baya-bayan nan aka daƙile hare-haren da kungiyar ADF ta kai kan majami’u da kuma wani mummunan harin da ta kai a wata makaranta a watan Yuni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com