Kiwon Fili: ‘Yan Bindiga Sun budewa Shanu Wuta a Jahar Anambra
An kashe Shanun makiyaya a jahar Anambra da sunan dabbaka dokar hana kiwo.
Wadanda suka budewa Shanun wuta ba jami’an gwamnati bane.
Mutan gari sun arce yayinda suka ji karar harbin bindiga.
Anambra – Wasu yan bindiga sun bindige wasu Shanu dake kiwo a garin Oba, karamar hukumar Idemili-South a jahar Anambra.
Read Also:
Makiyayan dake kiwon Shanun da mutanen gari sun arce yayinda yan bindigan suka fara kashe Shanun, masu idanuwan shaida suka bayyanawa Sahara Reporters.
A cewar wani mai idon shaida, yan bindigan sun kashe Shanun ne da sunan dabbaka dokar hana kiwo a fili a jahar; duk da cewa ba’a kafa dokar hana kiwo a jahar Anambara ba tukun.
Yan majalisar dokokin jahar sun fara tattaunawa kan dokar ranar 22 ga Satumba.
Zaku tuna cewa a ranar 11 ga Mayu, gwamnonin kudancin Najeriya sun yi ittifakin haramta kiwo a fili a yankin.