Gwamnatin Jihar Kogi na Shirin ɗaukar ‘Yan sa-kai 1,050 Aikin Tsaro

 

Gwamnatin jihar Kogi na shirin ɗaukar ‘yan sa-kai 1,050 da zimmar kyautata tsaron jihar da ke tsakiyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa an ɗauki matakin ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da buƙatar da gwamnati ta gabatar mata yayin zamanta na yau Laraba.

Tun da farko, Kwamashinan Ƙananan Hukumomi Salami Ozigi-Deedat ya aika wa majalisar wasiƙar neman amincewarta na ɗaukar mafarauta 50 daga kowace ƙaramar hukuma 21 na faɗin jihar.

Gwamnatin ta bayyana ƙarancin jami’an tsaro a matsayin babban dalilin ɗaukar mafarautan aiki.

Bayan amincewar da suka yi, ‘yan majlisar sun ba da umarnin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ne za su ɗauki nauyin biyan albashin dakarun a yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here