NCMPI ta Koka Kan Kisan Gillar da Aka Cigaba da yi a Jahar Plateau
Shugaban kungiyar samar da zaman lafiyan musulmai na arewa ta tsakiya, Alhaji Saleh Zazzaga ya koka akan kisan da aka cigaba da yi a jahar Filato.
Ya bukaci jami’an tsaro da su sanya ido matuka kuma su tabbatar sun cigaba da kulawa da dukiya da rayukan jama’an jahar wacce take da iyaka da Kaduna ta kudu.
Ya roki jami’an tsaro akan mayar da hankulansu wuraren Jos zuwa Bukuru don gudun bata-gari su cigaba da kaiwa mutanen da basu ji ba basu gani ba hari.
Jos, Filato – Shugaban kungiyar samar da zaman lafiyan musulmai na arewa ta tsakiya (NCMPI), Alhaji Saleh Zazzaga ya koka a kan kisan gillar da ake cigaba da yi a wasu wurare a jahar Filato.
Read Also:
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya roki jami’an tsaro a kan su mayar da hankulansu kacokan kuma su tabbatar sun cigaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’a mazauna garuruwan da suke da iyaka da kudancin jahar Kaduna.
Zazzaga ya yi bayani dalla-dalla
A wata hira da manema labarai sukayi da Zazzaga a ranar Juma’a, ya ce shugabannin addinai na musulunci da kirista su mike suyi iyakar kokarin ganin su janyo hankalin jama’a don dawo da zaman lafiya saboda mabiyansa suna bin duk abubuwan da suka ce.
Ya roki jami’an tsaro akan su mayar da hankulansu wuraren Jos zuwa Bukuru yadda bata-gari za su daina cigaba da kaiwa mutanen da basu ji ba basu gani ba hari, Daily Trust ta rawaito.
Ya yabawa yadda gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ya tsaya tsayin-daka wurin kama bakin zaren da kuma daukar tsauraran matakai a kan dakatar da rikicin wanda idan banda sa bakinsa da yanzu al’amarin ya faskara.
Zazzaga ya yi kira ga shugabannin gargajiya da mazauna yankuna da suyi gaggawar bayyana masu daukar doka a hannunsu a anguwanninsu saboda jami’an tsaro su kawo dauki.