Mun Dade da koran Kabiru Marafa- APC
Babban jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman ya ce sun dade da korar Sanata Kabir Marafa daga jam’iyyar.
Liman ya ce tun a shekarar 2019 suka dakatar da Marafa saboda yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Ya yi zargin cewa Marafa baya nufin APC da alkhairi duba ga abubuwan da yake yi don haka jama’a su daina kallonsa a matsayin dan jam’iyyar Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman, ya ce Sanata Kabiru Marafa ba dan jam’iyyar bane.
Liman ya ce: “Har yanzu Marafa korarre ne. Tun a shekarar 2019 jam’iyyar ta kore shi.”
Read Also:
Liman ya bayyana haka yayinda yake martani ga kalaman da aka alakanta da Marafa, inda yake zargin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa da rashin adalci, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce: “A iya saninmu dai APC a Zamfara ta sallame shi, tun a 2019. “Mun sallame shi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar sannan kuma mun gabatar da hukuncinmu zuwa ga hedkwatar APC ta kasa, Abuja.
“Don haka muna kira ga jama’a a kan kada su dauke shi a matsayin dan APC.
“Bama kallon Marafa a matsayin dan cikinmu saboda jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party na amfani da shi wajen haddasa manakisa a jam’iyyar.
“Kin biyayya ga hukuncin kwamitin uwar jam’iyyar ta kasa ya isa dalili na sanin cewa Marafa baya nufin APC da alkhairi.”