Wasu ‘Yan Bindiga Sukai wa Tawagar Wani Kwamishina Hari

Ƴan bindiga sun kai wa tawagar gwamnatin Jihar Zamfara hari.

Direba ɗaya daga cikin tawagar ya riga mu gidan gaskiya.

Tawagar tana dawowa ne daga Jihar Katsina inda ta tafi mika yara da mata da aka ceto da masu garkuwa Ƴan bindiga sun afka wa tawagar gwamnatin jihar Zamfara a hanyarsu ta dawowa daga Jihar Katsina.

Tawagar ta tafi Katsina ne don mika wa gwamnatin Jihar mata da yara fiye da 26 da aka ceto daga hannun masu garkuwa.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

“A ranar 9 ga watan Nuwamba misalin ƙarfe 10 rundunar yan sanda ta samu rahoton cewa tawagar gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin kwamishinan tsaro da ayyukan cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran ta fuskanci barazana sakamakon musayar wuta da kungiyoyin ƴan bindiga biyu keyi a Dogon Ƙarfe, Gidan Jaja titin Zurmi – Jibiya a ƙaramar hukumar Zurmi.

“Tawagar na dawowa daga Jihar Katsina ne bayan mika mata da yara fiye da 26 da aka sace a ƙaramar hukumar Faskari da gwamnatin Jihar Zamfara ta ceto a shirinta na sulhu da ƴan bindiga.

“Direba ɗaya daga cikin tawagar ya mutu.

Nan take ƴan sanda da sojoji sun isa wurin inda suka yi wa tawagar rakiya,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here