Fiye da kashi 42% Cikin 100% na ‘Yan Koriya ta Kudu Masu Shekaru 30 ba su yi Aure ba

 

Sabbin alkaluman kidaya sun nuna cewa ana cigaba da samun matukar raguwa a yawan masu yin aure a kasar Koriya da kudu duk da kamfe da gomnati ta ke yi na yin kira ga matasa da su yi aure, su haifi yara.

Fiye da kashi arbain da biyu cikin dari na ‘yan koriya ta Kudun masu shekaru talatin ba su yi aure ba abinda ke nuni da cewa adadin wadanda ba su yi aure a kasar ya karu da kashi shida a cikin shekaru biyar da suka gabata .

Wakiliyar BBC ta ce matasa da dama a Koriya ta Kudu sun jingine yin aure da haihuwa saboda matsalar rashin aikin yi da tsaddar gidaje.

Wannan ya sa Koriya ta kudu ta zama kasa mai mafi karancin masu haihuwa kuma ta samu matukar karuwa a yawan tsofaffi a jerin kasashen duniya da suka cigaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here