Korona: Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Ranar Litini
Ko shakka babu yanzu, an shiga babin annobar korona 2.0.
Bayan fiye da mako daya jere, an samu adadin sabbin masu kamuwa kasa da 500 a rana.
Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa kuma an dakatad da bukukuwan Kirismeti.
Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.
Read Also:
Mutane 397 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 84,811 a Najeriya.
Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 71,357 yayinda 1264 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin jihohin da adadin wadanda suka kamu:
Lagos-144
Plateau-83
Kaduna-48
Adamawa-36
Rivers-22
Oyo-16
Kebbi-10
Nasarawa-7
Sokoto-7
FCT-5
Kano-5
Edo-4
Jigawa-3
Ogun-2
Akwa Ibom-2
Niger-1
Bauchi-1
Zamfara-1