Kogi: Kotu ta Umarci Jahar Da ta Biya Korarren Mataimakin Gwamnan
Kotun masana’antu ta kasa, da ke zama a Abuja ta umarci gwamnatin jihar Kogi da ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar N180,000,000.
A watan Oktoban 2019 ne ‘yan majalisar jihar suka tsige Simon Achuba daga matsayin mataimakin gwamna a bisa zarginsa da rashin da’a.
Bayan tsige shi ne ya maka gwamnatin a kotu, inda ya bukaci ta biya shi kudadensa da ba a ba shi ba lokacin yana mataimakin gwamnan jihar Kotun masana’antu ta kasa da ke zama a Abuja, ta umarci gwamnatin jihar Kogi, da ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar, Simon Achuba, naira miliyan 180.
Read Also:
Alkalin kotun, mai shari’a Oyebiola Oyewunmi, ya umarci gwamnatin jihar da ta biya kudin cikin kwanaki 30 da ribar kaso 30 bisa dari na kowanne wata.
Kotun ta share wa Achuba hawayensa, inda ta bukaci a biya shi naira miliyan 328.32,000 a matsayin ribar da ta hau kudin.
Ya bukaci a biya shi N921,572,758 na tsaron lafiyarsa, kudin tafiye-tafiye, da sauran kudaden da yakamata a biya shi lokacin yana mataimakin gwamnan jihar.
‘Yan majalisar jihar Kogi sun tsige Achuba a watan Oktoban 2019, Punch ta wallafa.
Bayan sun tsigeshi, sun mika rahoto ga shugaban alkalai, Alkali Nasir Ajana, don yayi bincike a kan zargin rashin da’ar tsohon mataimakin gwamnan.