Kotun ɗaukaka ƙara Rashen Jihar Kano ta Dakatar da Hukuncin Soke Nasarar Jam’iyyar Labour a Jihar Abia

 

Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya rashen Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yi na soke nasarar Zaɓaɓɓen Gwamnan Abia Alex Otti.

Kotun ta bai wa gwamnan damar ɗaukaka ƙarar a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ƙarar ta shafa a gaban Mai Shari’a Mohammed Yunusa ranar 18 ga watan Mayu.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa tawagar alƙalai uku ta kotun ta bai wa gwamnan mai jiran gado wa’adin kwana bakwai na ɗaukaka ƙarar.

Kotun ta ba da umarnin ne har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙarar da za a ɗaukaka.

Sai dai kuma ta ce ɓangaren gwamnan zai biya waɗanda yake ƙara tarar naira miliyan biyu kowannensu idan har suka gaza ɗaukaka ƙarar kamar yadda ta zayyana musu.

Tun farko dai wani mai suna Ibrahim Haruna ne ya shigar da ƙarar yana ƙalubalantar nasarar jam’iyyar Labour a Abia da kuma zaɓen fitar da gwani da ta gudanar a Jihar Kano.

Kotun ta amsa buƙatarsa kuma ta soke dukkan ‘yan takarar da suka shiga zaɓe ƙarƙashin tutar jam’iyyar a Kano da kuma Abia, ciki har da Alex Otti da ya lashe zaɓen gwamna a Abia, saboda ba a bi ƙa’idojin dokar zaɓe ba.

Jibrin wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP kuma ya yi nasarar lashe zaɓen majalisar wakilai, ya ce Tinubu da Kwankwaso sun gana ne domin tattauna yadda za su yi aiki tare domin haɗin kai da ci-gaban ƙasa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here