Ibadan: Kotu ta Datse Igiyar Auren Shekara 10
Matar aure ta zargi mijinta da sace mata ‘yan kudadenta da ake boyewa a ma’adanarta.
Bayan zargin sata, matar mai suna Shakirat ta yi zargin cewa mijinta ya na yi mata barazanar cewa zai watsa mata ruwan asid – Alƙali Ademola Odunade, shugaban kotun al’adu ta Mapo da ke Ibadan, ya warware igiyar auren don wanzuwar zaman lafiya.
Kotun al’adu da ke yankin Mapo a Ibadan ta datse igiyar auren da ya shafe shekaru goma tsakanin wani ɗan achaɓa, Akinola Olaogun, da matarsa, Shakirat, sakamakon zargin halin bera da barazanar watsa mata ruwan asid da ya ke yi.
Da yake yanke hukunci, alƙali Ademola Odunade, shugaban kotun ya warware igiyar auren don wanzuwar zaman lafiya a tsakaninsu.
Read Also:
Odunade ya raba ƴaƴan su guda biyar inda ya miƙawa Olaogun ƴaƴansu guda biyu na farko yayin da Shakirat ta karɓi guda ukun ƙarshe.
Kazalika, ya kuma gindayawawa Olaogun sharadin biyan dubu sha biyar ₦15,000 duk wata a matsayin kuɗin ciyar da yaran.
Da farko, an zargi Olaogun da yi wa matarsa barazana da cewa zai watsa mata ruwan acid saboda ta gudu, ta barshi, zuwa wurin masoyinta da suke rayuwa tare. Daga bisani, Olaogun ya amsa, a gaban kotun, cewa yana dukan matarsa.
“Mai Shari’a, gaskiya ne nayi barazanar watsa ruwan acid ga matata da kuma babarta, amma barazana ce kawai don su ji tsoro ba wai hakan nake nufi da gaske ba,” a cewarsa
Shakirat ta roƙi kotun ta amsa addu’arta ta neman a raba aurensu, don ganin ra rabu da ƙaya. “Yana dukana kuma yana yi min barazanar wanka da ruwan asid. Yana satar kuɗi daga ma’ajiyata. “Daɗin daɗawa shi manemin mata ne, kuma bai san ciwon kansa ba”, kamar yadda Shakirat ta faɗawa kotu.