Me ya sa ƙungiyar ASUU ta ƙi janye Yajin Aiki?

Ɗaliban jami’a a Najeriya na ci gaba da jiran tsammani bayan shafe watanni bakwai suna zaman gida saboda yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’in ta ASUU.

Tun a ranar 23 ga watan Maris kungiyar ASUU ta fara yajin aikin sai baba ta gani, saboda dagewar da gwamnati ta yi wajen aiwatar da tsarin albashi na IPPIS wanda ta ce dole ne dukkanin malaman jami’a su amince da shi.

Ƙungiyar ASUU ta dage kan cewa tsarin biyan albashin IPPIS, shi ne babbar matsalarta, kuma idan har gwamnati ba ta yi wani abu a kai ba, to malaman jami’oi za su ci gaba yajin aiki.

Makwanni biyu da suka gabata an ga alamun cewa za a iya kawo karshen yajin aikin, bayan kalaman gwamnati na cewa za ta duba yiwuwar amincewa da wani tsarin albashi da kungiyar ASUU ke son ɓullo da shi a madadin IPPIS.

Tsarin IPPIS da aka samar a karkashin ofishin babban akanta janar na kasar na da manufar riƙa biyan dukkan ma’aikatan gwamnatin albashinsu kai-tsaye zuwa asusun ajiyarsu na bankuna, tare da sanya idanu kan yadda ake cirar kudin ma’aikatan kasar.

To sai dai fatan da ake da shi na cewa ɗaliban jami’a za su koma don ci gaba da karatu ya zo karshe a ranar lahadin da ta gabata, saboda yadda aka kasa fahimtar juna tsakanin gwamnatin da kungiyar ASUU game da tsarin da ake son a rika amfani da shi.

Matsayin gwamnati

Rahotanni sun an ambato ƙaramin ministan ilimi Emeka Nwajiuba na sukar ƙungiyar ASUU, yana mai cewa sun kasa fahimtar bukatun malaman jami’oin.

Gwamnati ta zargin kungiyar ASUU da rashin tsayayyar manufa a yayin tattaunawa, tana cewa kungiyar ba ta da alkibla a manufofin da take son cimmawa.

Ministan ya shaida wa manema labarai cewa ƙungiyar ASUU na sa son rai ga batun tsarin albashin na IPPIS da ke adawa da shi, zargin da ƙungiyar malaman ta musanta kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Karamin ministan ya ce sun kasa fahimtar takamaimai abin da kungiyar ke nufi da ta shafe kusan watanni bakwai tana gudanar da yajin aikin da take yi.

An kuma ruwaito ministan na cewa yanzu gwamnati ta kasa fahimtar manyan buƙatun ASUU, musamman waɗanda suka fi muhimmanci a biya wa ƙungiyar.

Ya ce gwamnati ba za ta haɗe tsarin biyan albashi ƙungiyar ASUU ba da IPPIS har sai an gwada tsarin.

Tun da farko gwamnati ta buƙaci malaman jami’oin yin rijista da tsarin domin samun albashi, yayin da suke shirya nasu tsarin albashin.

Buƙatun ASUU

A ranar 23 ga watan Maris ƙungiyar ASUU ta tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani kan dagewar da gwamnati ta yi na aiwatar da tsarin albashi na IPPIS, wanda gwamnati ta ce dole dukkanin ma’aikatu su rungume domin biyansu albashi

Baya ga adawa da tsarin albashin na gwamnati, ƙungiyar malaman ta zargi gwamnati da ƙin mutunta yarjejeniyar da suka amince a shekarun baya.

Farfesa Haruna Musa shi ne shugaban ASUU reshen jami’ar Bayero Kano, kuma a baya-bayan nan ya shaida wa BBC irin buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.

Farfesan ya ce sun jima suna yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan bukatun da suke son a biya musu, amma har yanzu ta gaza aiwatar da su.

Ya ce,”Abubuwan da suke cikin yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin, abubuwa ne wadanda idan aka bi su ko shakka babu jami’o’in kasar za su dawo hayyacinsu”.

Ga buƙatun na ASUU :-

Samar da wadatattun kudi wanda za a yi ayyuka domin farfado da jami’oi.

Da biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekara biyar zuwa shida ba a biya ba

Da matsalar yadda jihohi ke kirkirar jami’o’i barkatai ba tare da yi musu tanadi na wadatattun kudade ba domin tafiyar da su.

Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami’o’in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu.

Da kuma batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS wanda shi ma ya zamo matsala babbaru.

 

Yaushe za a cimma matsaya?

Amsar da mutane da dama ke son ji kenan, sai dai a ƙashin gaskiya har yanzu tana ƙasa tana dabo.

Lokacin da aka yi tunanin kamar lamarin ya zo ƙarshe shi ne lokacin da gwamnati ta yi kamar za ta amince da tsarin da kungiyar ta bijiro da shi a madadin IPPIS, kafin daga bisani ta yi shuri da shi.

A halin da ake ciki, bangarorin biyu na ci gaba da sukar juna ne, da kuma kokarin wanke kai a wajen wadanda za su iya zargin cewa waninsu ne baya son a kawo ƙarshen kiki-kakar.

Yajin aikin ya fi shafar ɗalibai da suka shafe watanni a gida, lamarin da wasu ke ganin barazana ne ga makomar karatunsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here