Kotu ta Yanke wa Tsohon Shugaban Guinea, Camara ɗaurin Shekara 20 a Gidan Yari

 

An yanke wa tsohon shugaban mulkin sojan Guinea Moussa Dadis Camara hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari sakamakon kisan aƙalla mutum 156 a wani filin wasa da sojoji suka yi a watan Satumban 2009.

Sama da mata 100 aka yi wa fyade tare da raunata wasu masu zanga-zanga da dama yayin da suke nuna adawa da shawarar Camara ta tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2010.

Kyaftin Moussa Dadis Camara ya kasance tsohon shugaban ƙasa na farko a tarihin Guinea da aka gurfanar a gaban kotu.

An same shi tare da wasu mutum bakwai da ake tuhuma da laifin cin zarafin ɗan’adam.

Tun da aka fara shari’ar a shekarar 2022, Mista Camara ya musanta hannu a kisan kiyashin da aka yi a filin wasan kuma lauyansa ya bayyana hukuncin a matsayin bita-da-ƙullin siyasa, inda ya ce za su ɗaukaka ƙara.

Babu tabbas ko hukuncin na ɗaurin shekara 20 da aka yi wa Dadis Camara zai faranta wa waɗanda abin ya shafa rai, amma ana iya ɗaukarsa a matsayin muhimmin mataki na farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here