Jam’iyyar Islama ta Karama: Kotun Sojoji a Tunisia ta Daure ‘Yan Majalisar Dokoki 2
Wata kotun sojoji a Tunisia ta daure wasu ‘yan majalisar dokoki biyu daga jam’iyyar Islama ta Karama.
Read Also:
An zargi Nidal Saudi da cin mutuncin ma’aikatan tsaro a filin jirgin sama, kuma an hukunta Saif Eddine Makhlouf saboda yi wa alkali barazana da kuma yin wasu kalamai a kotu.
Mista Makhlouf yana yawan sukar shugaban Tunisia, Kais Saied.
Kwanan nan shugaban ya dakatar da majalisar kuma ya kwace kusan dukkan iko a hannunsa, lamarin da ya haifar da karuwar damuwa game da tabarbarewar hakkin dan adam a kasar.