Kotu ta Gurfanar da Wani Dan Majalisa
Kotun majistare da ke yankin Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba majalisar wakilai daga mazabar Billiri/Balanga a jihar Gombe, Mista Victor Mela.
– Rundunar ‘yan sanda a birnin tarayya ta rubuta korafin zargin Mista Mela da rantsuwa a kan karya yayin da ya cike fom din INEC
– Lauyan da ke kare dan majalisar ya bukaci kotu ta yi sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan Mista Mela
Wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba a majalisar wakilai, Mista Victor Mela, bisa zarginsa da bayar da bayanan karya ga hukumar zabe ta kasa (INEC) tare da yin rantsuwa a kan cewa gaskiya ne.
Read Also:
Kotun ta ce dan majalisa Mela, mai wakilatar mazabar Billiri/Balanga a majalisar tarayya, ya bawa INEC bayanan karya domin samun damar tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
Hukumar ‘yan sandan birnin tarayya (FCT), Abuja, ce ta gurfanar da Mista Mela bayan zarginsa da rattaba hannu, a matsayin rantsuwa, a kan bayanana karya da ya bayar yayin cike fom din hukumar INEC mai lamba CF001 gabanin zaben 2019
Alkalin kotun da ya saurari karar ya saka ranar yanke hukunci a kan karar bayan lauyan da ke kare Mista Mela ya nemi kotu ta yi sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan wanda ya ke karewa.
Hukumar INEC ta bayyana Mista Mela a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben kujerar zaben dan majalisar wakilai na mazabar Billiri/Balanga a zaben da aka gudanar a cikin watan Fabarairu na shekarar 2019.
Duk da Ali Isa, dan takarar jam’iyyar PDP, ya kalubalanci nasarar da Mista Mela ya samu a zaben, kotun turabunal da ta daukaka kara da ke Jos sun jaddada nasarar da dan takarar na APC ya samu.