Sace Alkur’ani: Kotun Kano ta Yankewa Barawon Hukuncin Share Masallaci na Tsawon Kwanaki 30

 

A birnin Kano, an yanke wa wani mutum hukuncin share masallaci na tsawon kwanaki 30 a jere.

An yanke masa hukuncin ne bisa zarginsa da aka yi shiga masallaci tare sace Alkur’ani gida takwas.

Wanda aka hukunta da kansa ya amsa laifinsa bayan da aka gurfanar da shi a gaban wata kotun shari’a.

Kano – Wata kotun shari’a da ke zama a Fagge ‘Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.

Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur’ani guda takwas.

Sai dai jami’an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, Daily Nigerian ta ruwaito.

An gurganar dashi a gaban kotu Don haka masu gadin sun mika shi ga ofishin ‘yan sanda na Filin Hockey, wanda a ranar Talata ya gurfanar da shi a kotun Shari’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki?

Ka tuntubemu a [email protected]! Lokacin da mai gabatar da kara na ‘yan sanda, Abdul Wada, ya karanto tuhumar da ake yi wa Abdullahi, nan da nan ya amsa laifinsa.

Don haka alkalin kotun, Bello Musa-Khalid, ya yanke masa hukuncin share farfajiyar babban masallacin Juma’ar Fagge, na tsawon kwanaki talatin a jere.

Rahoto na cewa ana kallon masallacin Juma’a na Fagge a matsayin mafi girma a jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here