Kotu ta Bada Izinin Kamo Mata Wani Farfesa

Kotu ta bada umarnin a kamo mata Farfesa Ignatius Uduk a Akwa Ibom.

Hukumar INEC ta na zargin Ignatius Uduk da taba mata alkaluman zabe.

A baya an bukaci Farfesan na jami’ar Uyo ya bayyana gaban INEC, ya ki.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa babban kotun jihar Akwa Ibom da ke zama a garin Uyo, ya bada umarnin a cafke Farfesa Ignatius Uduk.

Alkalin ya bada wannan umarni ne kwanaki kadan bayan wani kotu da ke zama a garin Ikot- Ikpene, ya gurfanar da wani Farfesan, Peter Ogban.

Shi ma Ignatius Uduk wanda ya fito daga jami’a daya da Peter Ogba, hukumar zabe na kasa, INEC tana zarginsa da hannu a laifin magudin zabe a 2019.

INEC ta na zargin Peter Ogban da taba sakamakon zaben da bai cikin wadanda su ka yi aikin tattara wa.

Hukumar mai zaman kanta ta fitar da jawabi ta bakin shugaban sashen wayar da kan jama’a game da sha’anin zabe, Odaro Aisien, game da shari’ar.

Odaro Aisien ya ce INEC ta yi kokarin zama da Farfesa Peter Ogban, amma abin ya faskara duk da an yi ta aika masa takardu ta jami’arsa ta UNIUYO.

Aisien ya ke cewa INEC ta tafi kotu bayan Farfesan ya yi watsi da takardar da aka rika aika masa.

A karshe Alkali ya duba bukatun INEC, ya bukaci wanda ake nema ya hallara gaban kuliya a ranar 18 ga watan Nuwamba, duk da haka ya ki zuwa kotu.

Ganin abin ya faskara, sai Lauyan hukumar INEC, Kpoobari Sigalo, ya roki kotu ta sa a cafke Ogban, Lauyan ya ce an kuma amince da wannan rokon.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here