‘Yan Sanda Sunyi Fito na Fito da ‘Yan Bindiga

Wasu ‘yan sandan jihar Katsina sun yi musayar wuta da wasu ‘yan bindiga a dajin Rugu.

Sun samu nasarar ceto wata mata mai shekaru 55, sannan sun harbi wasu ‘yan bindigan.

Da ‘yan sandan suka shiga daji bincike, sun ga wasu babura guda 2 marasa lamba.

A ranar Litinin ‘yan sandan jihar Katsina suka yi musayar wuta da ‘yan bindiga a karamar hukumar Safana yayin kokarin ceto wata mata mai shekaru 55, Hafsatu Idris.

An samu labarin yadda ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Gamma wuraren karfe 1, lokacin da suka saci Hafsatu, jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce, “Rundunar Operation Puff Adder sun yi musayar wuta a tsaunin Habul da ke dajin Rugu wuraren karfe 4:20 na asuba, inda suka yi bata-kashi da masu garkuwa da mutanen har suka ceci matar.”

A cewar Gambo, “Rundunar ta samu damar ceto wacce aka yi garkuwa da ita, da kuma wasu babura 2, kirar Bajaj marasa lamba.

“Da yawan ‘yan ta’addan sun tsere cikin dajin da raunuka, don sun ga jini sosai a dajin. “Yanzu haka ‘yan sandan suna zagaya dajin ko za su tsinci gawawwaki ko kuma ‘yan ta’adda masu rauni, don a samu damar yin bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here