Kotu Ta yi Min Rashin Adalci – Ndume

 

Jiya da misalin karfe 4 na yamma aka tafi da Sanata Ndume gidan gyaran hali da ke Kuje, Abuja.

Amma kuma lauyansa ya ce ba a basu wasu takardu da suka bukata ba domin su daukaka kara.

A yau ne ake sa ran za a cigaba da shari’ar, wala Alla ko zai samu dama cika wani sharadi a sakeshi.

Sanata Ali Ndume, wanda ma’aikatan gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, suka tafi da shi a ranar Litinin, a bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja, zai daukaka kara akan hukunci da aka masa yau, Talata.

Lauyan Ndume, Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, Daily Trust ta tabbatar.

A cewarsa, ba a ba iwa Ndume damar jin ta bakinsa ba, sannan ba su bashi wasu takardu da ya bukata ba don ya kare kansa.

Alkali Okon Abang, wanda shine ya bayar da wannan umarnin a kan Ndume, wanda ya tsaya wa tsohon shugaban PPRTT, Abdulrasheed Maina, da aka kama bayan Maina ya ki bayyana gaban kotu, bisa zargin cin kudin fansho na naira biliyan 2.

“Muna bukatar wasu takardu don gabatar da ita gaban alkali don kare Ndume,” cewar lauyansa.

“Ba a yi mana adalci an bamu wannan damar ba, kafin kotu ta zartar da hukunci,” cewarsa. Wata majiya ta kusa da Ndume, ta ce an tafi dashi gidan gyaran halin da misalin karfe 4 na yammacin jiya.

Ya ce wayoyinsa ba sa tafiya, duk a kashe, tun bayan kotu ta bayar da umarnin tafiya dashi gidan gyaran halin.

“Za a koma da Ndume kotu yau don cigaba da shari’ar. Tunda kotu ta bayar da zabi 3, kuma muna fatan zai cikase ko da zabi daya ne don su sake shi,” kamar yadda majiyar tace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here